SUNNONIN JIMA,I

Sunnonin jima,i guda takwas  daduk wani masoyin annabi s.a.w yakamata yasani yakuma tuna dasu yakuma kiyaye yinsu sabida jima,i babbar ibadah ce amusulunci.

 koyi da annabi s.a.w ma  babbar ibada ce dakuma nuna tsantsan sonsa domin ibn kayyim allah byakjara masa yadda yataba cewa: hakikanin son annabi s.a.w shine koyi dashi acikin dukkanin lamura na rayuwar mutum, kwarai dukkan lamura domin babu wani abu da manzon allah s.a.w da musulunci ba tare da ya nuna mana ko ya koyar damu yan da yafi kamata muyisu ba abun daya rage mana kadai shine neman ilimin saninsu dayin amfani dasu. Dalilin dayasa kenan ma muka kawo muku wannan page din namu  dan tunatarwa akan kadan daga cikin muhimman abubuwa akan abun da annabi s.a.w da mulunci suka koyar akan jima,i  kuma munsan kai masoyin annabi s.a.w ne tun da har kake karanta wannan page din namu.

                                          sunnonin sun kasance kamar haka.

Ø  Na daya

Kiyaye tsaftar jiki data al,aura dayin wanka da gogi baki kafin fara jima,i.

Dakuma aske gashin al,aura akalla kasa da duk kwana arba,in

Ø  Na biyu

Yin jima,i ahalin da jiki yake adaidai da kuma nutsuwa.

Ayanayin da yake na matsannancin zafi ko sanyi, akuma yanayin da ciki ba,a yunwace yakeba kuma a cikin tsananin koshiba.

Ø  Na uku

Farawa da wasannin tayar da sha,awa masu zurfi!

 

 

Ø  Na hudu

                                yin addu,a kafun fara ainihin saduwa da iyalin.

Ø  Na biyar.

Jin tsoron allah ayayin saduwa da iyalin, ta hanyar kiyaye abubuwan da suke haramun.

Ø  Na shida.

Samun gamsuwarka ta hanyar halaliya da kuma tabbatar da samun gamsuwar iyalin taka.

Ø  Na bakwai.

Yin alwala ko wankar tsarkir yayin komawa zagaye na biyu idan kun bukata.

Ø  Na takwar.

Kawar da najasa ko wankar tsarki yayin gama jima,in, da kuma gaggauta yin wankan tsarki ko alwala.

Ø  Na tara.

Rufe sirrin abun daya faru na tsakanin ma,aurata na jima,in.

Ø 


Na goma.

Yana da kyau kar a tillasta yin jima,in ga wanda yake halin bacin rai, rashin lafiya, yunwa, ko  gajiya, ko bayan shan wani nau,in magani.

Sannan bashi da kyau yin jima,i atsaye ko yayin fuskantar alkibla ma,ana makaruhi ne.

Kadan daga sunnonin kenan atakaice.